Sojojin Kamaru Sun Fara Korar ‘Yan Najeriya Daga Bakasi

kauyukan Bakassi. (VOA / S. Olukoya)

Sojojin kasar Kamaru sun fara korar ‘yan kasuwar Najeriya dake tsibirin Bakasi, wadanda ake zargi da kni biyan haraji.

Sojojin kasar Kamaru sun fara korar ‘yan kasuwar Najeriya dake tsibirin Bakasi, wadanda ake zargi da nokewa suki biyan haraji.

Kamaru ta sami cikakken iko da wannan yankin ne mai cike da arzikin man fetur a cikin watan Agusta shekara ta dubu biyu da goma sha uku bayan wani hukumcin da kotun kasa da kasa ta yanke. Amma kashi casa’in bisa dari na mazauna yankin ‘yan Najeriya ne.

Wani mazaunin yankin da wakilin Muryar Amurka mai aiko da rahotonni daga yankin Bakassi Moki Edwin Kindzeka ya yi hira da shi, ya bayyana cewa, an kafa dokar hana fita a tsibirin bayan wata hatsaniya tsakanin wadansu ‘yan kasuwa da gungu-gungun masu karbar haraji. Yace ‘yan kasuwar sun kasa fahimtar harajin da kasar Kamaru ta saka. Bisa ga cewarshi, wani lokaci bayan karamar hukuma ta karbi haraji daga hannun ‘yan kasuwar sai kuma jami’an haraji su zo da ‘yan sanda suna neman su karbi wani haraji,

Ga Ibrahim Ka-Almasih Garba da fasarar rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton Korar Yan Najeriya Daga Bakassi