Sojojin Isra'ila sun kai wani hari na ba-saban ba yau Talata a Zirin Gaza wanda ya yi sanadin kisan wani babban kwamandan wata kungiyar masu zafin kishin addinin Islama.
Wata sanarwa daga ofishin Firayim Minista Benjamin Netanyahu ta ce Bahaa Abu el-Atta shi ne ya kai wasu hare-haren ta'addanci da yawa, da kuma harba wa Isra'ila rokoki a cikin 'yan watannin nan, kuma ya kudiri aniyar kai wasu hare-haren.
Kungiyar mayakan ta ce harin da Isra’ila ta kai ya kuma yi sanadiyar kisan matar Abu el-Atta, bayan haka ya raunata ‘yayansu.
Kungiyar ta lashi takobin daukar fansa, kamar yadda kungiyar mayakan Hamas ita ma ta yi, wadda ta ce Isra’ila ce zata fuskanci duk wani sakamakon da zai biyo baya akan wannan mummunan farmakin da kuma yadda take kara aunasu.
Mayakan Falasdinawa sun mayar da martani akan matakin da Isra’ila ta dauka ta hanyar harba mata rokoki.