Sojojin Iraqi sunce sunyi nasarar kame wasu daga cikin muhimmam wurare da suka hada da sansanin sojan saman dake arewacin kasar da ake takaddama akan sa na birnin Kirku, harma da filin jirgin, da kuma kanfanin mai da dai wasu sauran muhimmam wurare dake kusa da birnin.
Jami’an tsaron kasar dai sun sake karbe ikon wannan wurin ne daga mayakan kurdawa a yau littini biyo bayan kiran da Prime Minista Haider Al-Abadi yayi wa mayakan na gwamnati cewa su tabbatar sun tsananta tsaro a KirKuk.
A cikin sakon da ya aike musu Abadi yace yasan cewa ya zame wajibi gare shi da yayi abinda ya dace, biyo bayan kuri’ar jin ra’ayin jama’a da ya bayyana cewa kasar ta Iraqi na bisa siradi.
Gidan Talabijin na kasr ta Iraqi ya bayyana cewa sojojin gwamnati sun samu nasarar karbe muhimman wurare dake yankin lardin Kirkuk
Sai dai jami’an Kurdawa sun karyata wannan batu, amma dai sun amince cewa sojojin kasar na Iraqi sun dake da goyon bayan sojojin sa kai sun samu nasarar shiga Kirkuk ne kawai kuma suka karbe sansanin mayakan sama da kuma wasu rijiyoyin mai