Sojojin Hadin Gwiwa Tsakanin Amurka Da Nijar 8 Sun Mutu

An kashe sojojin Amurka 4 da dakarun Nijar 4 a lokacin artabo da 'yan kungiyar Islama.

Mukaddashin Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, Patrick Shanahan, ya amince da bayanan binciken harin da aka kai kan dakarun Amurka, na musamman da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Nijar, kusan shekaru biyu da suka gabata, wanda yayi sanadiyar mutuwar sojojin Amurka 4 da kuma sojojin Nijar 4.

A wata sanarwa da aka fitar da safiyar yau Alhamis, mukaddashin sakataren na harkokin tsaro, Shanahan, yace ya gamsu da “duk abubuwan da aka gano a binciken, kuma matakan da aka dauka sun yi dai-dai” bayan da yayi nazarin, rahoton binciken, na harin da aka kai ranar 4 ga watan Oktobar shekarar 2017, a kusa da kauyen Tongo-Tongo, mai kimanin kilomita 200 arewa da Yammai babban birnin Nigar.

Rahoton karshe, wanda aka fidda, a watan Mayun shekarar 2018, ya gano cewa akwai matsaloli da yawa da suka addabi dakarun, ciki har da rashin bada kyakkyawan horo, da kuma karancin kayan aiki masu kyau, gami kuma, da rashin shirin dakarun a lokacin da sojojin Amurka 46, da dakarun Nijar, suka kama hanyar neman wani babban dan ta’adda.