Shugabannin kungiyar Musulmin darikar sufuye sun mika kansu ga gwamnatin Somalia a jiya Asabar bayan wani fada da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22 a tsakiyar Somalia.
WASHINGTON DC —
Moallim Mohamud Sheikh shugaban harkokin addini a kungiyar da kuma Sheikh Mohamed Shakir shugaban Ahlu-Sunna Wal-Jamaa (ASWJ), suna rike a hannun sojojin gwamnatin Somalia a garin Dhusamareb, bayan da dakarun gwamnatin suka rinjayi mayakan kungiyar.
"Jami’an tsaron mu sun fafata a karshe kuma sun yi nasara kwace makaman mayakan Ahlu-Sunna, inji Osman Isse Nur mai magana da yawun sabon shugaban kasar, yana fadawa Muryar Amurka.
Da yake jawabi a wani faifan bidiyo da aka kafe a yanar gizo, shugaban na Ahlu-Sunna Wal-Jamaa Sheikh, Shakir yace sun amince kuma sun yi mubaya’a ga dakarun gwamnatin Somalia.