Sojoji Sun Ce Sun Sake Ceto Yara Da Mata Wajen 20 A Borno

  • Ibrahim Garba

Wasu sojoji a dajin Sambisa

Sojojin Najeriya sun yi ikirarin sake samun wata nasarar, inda har su ka kubutar da waasu mutane 20 akasari yara da mata

Shirin nan na tabbatar da kwanciyar hankali da ake kira ‘Operation’ Lafiya Dole a jahar Borno, ya kubutar da mutane wajen 20 a jahar ta Borno. Babban jami’in Hulda da Manema Labarai na shirin na Operation Lafiya Dole Kanar Tukur Gusau ya yi ma wakilinmu Haruna Dauda karin bayani bayan taron manema labarai.

Kanar Tukur Gusau ya ce Birget ta 21 da ke aiki a wuraren Bama ya yi sintiri ne yayin da ya samu nasarar kubutar da mutanen wadanda akasari yara ne da wasu mata hudu, bayan sun kashe ‘yan bindiga hudu. Y ace bayan haka ma sojoji sun gudanar da sintiri ta wuraren Sambisa, inda su ka ragargaza tungayen Boko Haram har su ka samu abubuwan harhada bama-baman Boko Haram.

Ya ce yanzu haka ma sun kama mutum biyu da rai kuma sun a cigaba da bincike.

Ga Haruna Dauda da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Sojoji Sun Ceto Mutane 20 A Borno - 3'51''