Mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar sojojin Kanal Tukur Gusau shi ya gabatar da matasan a ofishinsa dake garin Miaduguri.
A cikin bayanin da ya yi yace sun kama wani dan kungiyar Boko Haram ne sai suka sameshi da katin shaida na jabu da mutanen suka buga masa yayinda suke gudanar da bincikensa.
Binciken da suka gudanar ya kaisu ga inda mutanen masu buga katin suke.
Kanal Gusau ya ci gaba da yin bayani game da mutanen da suka cafke. Yace mutanen suna da naurori kala kala da kwamfutoci da pirinta da dai sauransu. Dan kungiyar Boko Haram da sojojin suka kama ya kaisu wurin mutanen da suka buga masa katin na jabu.
Bincikensu ya nuna cewa inda dan Boko Haram din ya kaisu aikin da suke yi ke nan na buga katin shaidar zama dan kasar Najeriya ga duk wanda ya biyasu musamman 'yan kungiyar Boko Haram.
Katin bogin da 'yan Boko Haram suke samu daga masu buga masu yana taimaka masu ta hanyar shige da fice ta yadda jami'an tsaro ba zasu ganesu ba.
Kanal Gusau yace duk shagon da suka kama yana buga katin shaida na bogi zasu hukumtashi saboda ceton rayukan al'umma.
Sojoji zasu mika mutanen da suka kama ga 'yansanda su cigaba da bincike kana su gurfanar dasu gaban kuliya.
Wani Malam Zakariya dake aikin kwamfutan kuma daya daga cikin wadanda aka kama yace a wajen kasuwancinsu aka kamasu. Ya musanta sanin dan Boko Haram din da aka kama da katin. Yace mutumin na biyu da aka kama shi mai aikin hoto ne. Shi ya kawo hoton ya buga masa katin bayan ya biyashi nera dari biyar.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.
Your browser doesn’t support HTML5