Sojoji A Kalla 11 Sun Mutu A Harin Kunar Bakin Wake A Pakistan

  • Ibrahim Garba

An kafa shingen bincike tun bayan harin kunar bakin wake a Kwarin Swat na Pakistan.

Da daren yau Asabar aka kai wani harin kunar bakin wake, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji akalla 11 a cewar hukuma. Amma kungiyar Taliban da ta kai harin ta ce sojojin da ta kashe sun fi haka yawa.

Wani harin kunar bakin waken da aka kai a wata tsohuwar tungar ‘yan bindiga da ke arewa maso gabashin Pakistan ya hallaka sojoji akalla 11 tare kuma da raunata wasu 13.

Harin ya auku ne da daren yau dinnan Asabar a kwarin Swat Valley, lokacin da sojoji ke wasu wasannin motsa jiki haka, a cewar wata takardar da aka fitar a hukumance.

Wani mai magana da yawun haramtacciyar kungiyar nan da aka haramta a Pakistan ta Taliban, y ace kungiyar ce ta aikata, y ace sojoji da dama sun mutu a wannan harin. To amma an san ‘yan bindigar da karin gishiri.