“Yadda siyasa ke tafiya yanzu, abin ya zama tamkar kasuwar biyan bukatun wasu tsiraru ne, domin manyan ‘yan siyasa na siyasar son zuci da kuma abinda za’a samu,” a cewar wani matashi mai suna malam Suleman Maraya Fagge.
Suleiman ya ce a yanzu siyasa babu bin ra’ayi, duk matashin da ke bin abinda uban gidansa ke yi, suna bin son zuciyarsu ne kamar yadda iyayen gidan keyi. Ya kara da cewa wani lokacin jahilci na taka rawa a siyasar matasa.
Ku Duba Wannan Ma Mahaifiyar Jaruma Nafisa Abdullahi Ta RasuMatashin na ganin cewar matasa da yawa na siyasar jahilci, da zarar sun sami ‘yan canji shi kenan, ba su damu da manufar dan takararsu ba.
“Akwai bukatar matasa su fahimci cewar jagororinsu ba sune a gabansu ba. Ya kamata su dinga maida hankali akan cancantar dan takara, don tabbatar da cewa mutun ne da ya san abinda ya keyi,” a cewar Suleiman.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5