Siriya Ta Ce Zargin Harin Gubar Da OPCW Ta Yi Ma Ta Bai Da Tushe

Gwamnatin Siriya ta yi watsi da wani rahoto da kungiyar dake sa ido akan makaman guba ta kasa-da-kasa ta fidda wanda ya gano cewa ta yiwu an yi amfani da sinadarin Chlorine wajen kai hari akan birnin Douma dake hannun ‘yan tawaye a karshen shekarar da ta gabata.

Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen Siriya da aka fidda jiya Alhamis ta ce rahoton na cike da bayanan da ba na gaskiya ba kuma ba shi da tushe.

Kungiyar haramta yin amfani da makaman guba da ake kira OPCW a takaice, ta fidda wani rahoto a makon da ya gabata wanda ya ce akwai hujjoji masu karfi da suka nuna cewa an yi amfani da wasu miyagun sinadirai dake dauke da Chlorine a harin da aka kai a watan Afirilun shekarar 2018.

Shaidun gani da ido da ma’aikatan lafiya a lokacin sun ce fiye da mutane 40 aka kashe a harin da aka kai.

Kungiyar ta OPCW ta kai ziyara Douma. Amma rahoton ta bai dora laifi akan yin amfani da gubar ba.