An bayana cewa Sinadarin Nukiliya, na da alfanu ka rayuwar dan Adam, ta fannoni daban-daban, kamar samarda makamashi, domin wutan lantarki, bunkasa Masana’antu, bunkasa harkokin noma da kuma amfani dashi wajen gano ma’adanai a karkashin kasa.
Farfesa, Sani Sambo, tsohon shugaban cibiyar Nukiliya, ta Najeriya, ne ya bayyana haka ga muryar Amurka, kasancewar yau ne ranar da majalisar dinkin duniya, ta ware domin a fafutukarta na ganin cewa an kauda sinadarin nukiliya, a doron kasa.
Ya ci gaba da cewa sinadarin na Nukiliya, na taimakawa wajen bincike-binciken kimiya, ya na mai cewa ko da yake dagwallon Nukiliya dashi ake yin makamin kare dangi wanda dalilin haka yasa majalisar ta dinkin duniya ke kokarin ganin cewa an kaudashi a doron kasa.
Your browser doesn’t support HTML5