Sifaniya Ta Fada Makoki Sakamakon Gagarumar Ambaliyar Ruwan Da Ta Hallaka Mutane 95

Spain Floods

Adadin mutanen da ambaliyar ta kashe shine mafi muni tun shekarar 1973 lokacin da aka kiyasta cewa wata ambaliya ta hallaka akalla mutane 150 a yankunan kudu maso gabashin Granada, Murcia da kuma Almeria.

Sifaniya ta fara gudanar da makokin kwanaki 3 a yau Alhamis a dai dai lokacin da masu aikin ceto dake amfani da jirage marasa matuka ke fafutukar zakulo masu sauran numfashi a ambaliya mafi muni da kasar ta taba gani a tarihi wacce ta yi sanadiyar salwantar rayuka 95.

An sauke tutoci kasa-kasa a gine-ginen gwamnati dake fadin kasar bayan da wata guguwa da ta taso daga tekun maditareniya ta haddasa mamakon ruwan sama da ambaliya mai cike da laka wacce ta yi awon gaba da mutane da motoci da gidaje.

Masu bada agajin gaggawa a bisa rakiyar sojoji 1, 200 na karade garuruwa da kauyukan da tabo ya yiwa kawanya domin ceto masu sauran numfashi tare da bude hanyoyin da karikitai suka rufe.

Manyan jami’an gwamnati sun yi gargadin cewar adadin wadanda suka mutu na iya karuwa sakamakon yawan mutanen da suka bata da kuma kasa shiga wasu yankuna da masu aikin ceto a jiya Laraba.

Sarki Felipe na 6 ya yi gargadin cewar har yanzu “ba’a fita daga yanayi na hatsari ba.”

Hukumar kula da yanayin Sifaniya (AEMET) ta sanya wuraren da ambaliyar tafi kamari dake yankin gabashin Valencia cikin wuraren da ake da kwakkwaran hasashen samun ruwan sama a yau Alhamis.

A kauyen Sedavi dake wajen yankin na Valencia, dan fansho francisco puente na kokarin share kwalla bayan daya kalli tulin sharar hargitsattsun motoci da titunan da suka lallace.

“Idan kaga lamarin, sai kace: “yanzu ni ke ganin wannan? mene ne hakan?” kamar yadda mutumin mai shekaru 69 ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na afp.

Adadin mutanen da ambaliyar ta kashe shine mafi muni tun shekarar 1973 lokacin da aka kiyasta cewa wata ambaliya ta hallaka akalla mutane 150 a yankunan kudu maso gabashin Granada, Murcia da kuma Almeria.