Shuwa Arab wasu kabila ne daga cikin kabilun da ke arewa maso gabashin Najeriya, musamman ta jihar Borno. Suma sun koka game da cewa suna cikin wadanda rikicin boko haram ya safa tare da farrakasu daga su har dabbobinsu da suke kiwo.
Sun koka game da cewa su kansu an sha sace musu mata da dabbobin amma ba kowa ma ya sani ba, domin kila hankalin jama’a bai kai kansu ban a tunanin kila abin ya shafesu. ‘Yan Shuwa din sun yi taron kungiyarsu ne a Borno tare da bayyana wasu jimilolin al’ummar da aka kashe musu ko kuma jikkata.
Kididdigar da suka bada ta tsawon kusan shekaru shida ne, akan Shanunsu da suka rasa sun ce ya kai sama da Shanu dubu dari da arba’in. ban da mutane sama da dubu daya da suka rasa rayukansu.
Kungiyar Alhaya ta Makiyayan ta bukaci gwamnatin Najeriya da su taimaka musu kamar yadda ake wa wadanda wannan abu ya shafa. Ga rahoton Wakilinmu Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5