Aung Sang Suu Kyi ta Kawo Ziyara Amurka

Myanmar Foreign Minister and State Counselor Aung San Suu Kyi is pictuired in a Bangkok airport in June 2016. (Reuters)

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya tarbi Aung Sang Suu Kyi wadda ake mata kallo tamkar shugabar Myanmar ce a fadar gwamnatin Amurka ta White House ranar laraba.

Obama ya nuna zakuwarsa domin ya saurari ra’ayinta dangane da yadda Amurka za ta dage takunkumi daga kan kasar da ke gabashin Asiya

Wannan itace ziyararta ta farko Amurka a matsayin Shugaba kuma firaminsta, matsayin da ta karba bayan jam’iyyarta tayi nasara a zaben da akayi a watan Nuwamba.

Kundin tsarin mulkin soji na kasar ya hana ta mukamin shugabancin kasar kasancewar tsohon mijinta da ya rasu da kuma 'ya'yanta ba 'yan kasa bane.

Aung San Suu Kyi ta shafe tsahon shekaru 20 tana daure gida a tsohuwar kasar da aka sani a da da Burma. Haduwarta da Shugaba Obama a Oval office ya kara tabbatar da cewa lallai ita ce dai shugabar fararen hula na kasar.