Shugabar Hong Kong Ta Yi Magana Kan Batun Masu Zanga-zanga

Shugabar yankin Hong Kong, Carrie Lam

Shugabar yankin Hong Kong Carrie Lam, ta ce tana fatan zanga-zangar lumana da aka yi akan titunan garin dake karkashin China, za ta zamanto wani sauyi cikin kusan watanni biyu da aka kwashe ana zanga-zangar nuna adawa da gwamnati.

Ita dai zanga zangar ta faro ne da nuna adawa kan wata doka da hukumomin yankin suka so su kirkiro, wacce za ta ba da damar a rinka tura wadanda ake tuhuma da aikata laifi zuwa China domin a yi musu shari’a, amma daga baya zanga-zangar ta juye zuwa tashin hankali ta kuma jefa Hong Kong cikin mummunan rikicin siyasa da ba a ga irinsa ba tun da Birtaniya ta mika ikon yankin ga China a shekarar alif 1997.

Masu zanga-zangar dai sun jera bukatocinsu da dama, ciki har da bukatar a janye kudirin aika masu laifi zuwa China baki ‘daya, a kuma kaddamar da bincike mai zurfi kan zargin cin zarafin da ‘yan sanda su kayi lokacin zanga-zanga, sai kuma wanke da sakin mutanen 700 da aka kama a lokutan zanga-zanga, da kuma dadadden buri na kaddamar da zaben shugaban yankin, tare da bukatar shugaba Lam ta yi murabus.