Shugabannin Kasashen Duniya Za Su Tattauna Akan Sauyin Yanayi

A yau Litinin shugabannin duniya zasu hadu a birnin New York dan hallartar taron Majalisar Kolin Kungiyar Majalisar Dinkin duniya, inda zasu tattauna akan sauyin yanayi duba ga yadda masana kimiyya suke gargadin a dau matakin kariya.

Kimanin Shugabannin kasashe 60 da Fira Ministoci ne ake sa ran zasu yi jawabai akan batutuwa da suka hada da yadda za a daina amfani da makamashin Coal a koma ga amfani da makamashin da bashi da illa ga yanayi, kiyaye aukuwa da magance masifu idan sun auku da zuba kudi a fannin yanayi a taron na wuni daya.

Shugaban Amurka Donald Trump bazai hallarci taron ba. A yau Litini, a maimakon haka, zai hallarci wani taro akan cin zarafi da ake yiwa mabiya addinai marasa rinjaye, musamman mabiya addinin Kirista, kafin ya zanta a zama daban-daban da shugabanin Pakistan, Poland, New Zealand, Singapore, Egypt da Korea ta Kudu.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guteres, ya kudiri jaddada wa shugabanin mahimmancin da wannan taron na yanayi yake dashi kuma ya kalubalance su da samar da kwakkwarar mafita ba kawai su tsara bayanai masu daukan hankali ba.

A gabanin taron da za ayi yau Litini, Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar da wani rahoto wanda cibiyar Lura da yanayi ta Duniya ta hada, mai nuna cewa an samu karuwar gurbtar yanayi da iskar Carbon, haurawar teku, dumamamar yanayi da kuma narkewar kankara.