Shugabannin Kasashen Afrika Na Ci Gaba Da taro A Kasar Mauritania

Shugabannin kasashen Afrika 30 na ci gaba da taronsu na kwannaki biyu da suka soma a kasar Mauritania inda suke kokarin tinkarar matsaloli da dama dake addabar nahiyar, ciki har da matsalar cin hanci, da maganar tsaro da kuma wahalhalun da jama’a kan abka cikinsu a sanadin tashe-tashen hankulla.

A jawabinsa na bude taron a jiya Lahadi, mai masaukin, shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ould (pron: ood) Abdel Aziz yayi wa takwarorinsa kashedi gameda sakaci akan harakar tsaro, a daidai lokacinda ake bada rahoton cewa an kashe wasu mutane fararen hula hudu a wani harin da aka kaiwa wata bataliyar sojan Faransa dake aiki a kasar Mali.

Haka kuma shugaban ya gaya musu cewa idan basu ja wa matsalar cin hanci da rashawa burki ba, zai yi wuya Afrika ta sami ci gaba a fuskar tatalin arziki.

Sauran batutuwan da ake sa ran shugabannin na Afrika zasu taba a lokacin taron kolin nasu zasu hada da kokarin sulhunta rikittan siyasan dake abkuwa a Sudan ta Kudu da kuma sulhun da ake fatar ganin an samu tsakanin Ethiopia da Eritrea. Akwai kuma maganar zabukka masu zuwa da za’a yi a kasashen Mali, Kamaru, Congo-Kinshasha da kuma Zimbabwe.