Shugabannin kasashe da dama za su hadu gobe Lahadi a birnin Berlin na kasar Jamus, don duba yadda za a kawo karshen rikicin kasar Libiya, da kuma yadda za a sa bangarorin da ke rikicin su sake kama tafarkin sasantawa, wadda ta sukurkuce sanadiyyar sake barkewar rikici a watan Afirilun bara.
Sakatare-Janar na MDD zai je babban birnin na kasar Jamus ya hadu da Shugabannin Burtaniya da Faransa da Jamus da kuma sakataren harkokin wajen Amurka da dai sauran masu ruwa da tsaki. Za su yi kokarin sasanta Firaminista Fayez Al-Serraj da duniya ta amince da shi da kuma jagoran ‘yan tawaye Janar Khalifa Haftar.
Manufar wannan hobbasar ita ce a cimma kwance damara, sannan a yi amfani da tsagaita wutar wajen sasanta dukkan bangarorin kasar kai tsaye kuma daki-daki.