Duk wadanda aka kama da satar mutum, satar shanu da fashi da makami matasan Fulani ne.
Wani shugaban Fulanin yace abun da ya lura dashi shi ne su tsaya tsayin daka su dakile wadannan ayyukan asha da suka addabesu saboda sace sace da kashe kashe, duk wanda aka kama bafillatani ne.
Satar shanu da satar mutane domin samun fansa ya zama tamkar ruwan dare gama gari a jihar ta Taraba lamarin da ke sa mutanen jihar zaman dar dar.
Taron ya hada da makiyayan jihar da wasu ma daga waje domin lalubo bakin zaren matsalolin da suke fuskanta.
Muhammad Mafindi Umar Dan Buram mai ba shugaban kungiyar Miyetti Allah shawara akan harkokin kiwo kuma shugaban Miyetti Allah na jihar Taraba yace makasudin taron domin su duba abubuwan da suka shafesu suka zama masu illa a rayuwar bafillatani da nufi dakilesu.
Yace sun damu da yadda ake sace shanu da sace mutane da kuma fashi da makami. Ana sace mutane a boyesu sai an biya diya.
Yace taro ya yi kyau. Duk wakilan Fulanin jihohi goma sha shida dake Taraba sun hallara. Sun yadda yanzu su je su ja kunnuwan 'ya'yansu cewa dan bafullatani basu yadda ajishi a harakar sata ba.
Baicin hakan Fulanin zasu sa rana su raba goro su sauke Kur'ani ranar domin kawo karshen duk wani mugun hali na matasansu.
Shi kuwa Ardo Husseini Yusuf Boso mataimakin shugaban kungiyar Fulani ya yabawa jihar Taraba bisa yunkurin da suka yi.makiyaya. Yana fatan 'ya'yansu zasu ji tsoron Allah su bar sata da fashi da makami domin basu iske iyayensu cikin sata ba.
Ya kira gwamnatoci su wayar da kawunan Filani kuma su inganta ilimin yaran Fulani domin a samu sassauci a kasar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5