Al'ummar Fulani sun yi babban taro domin fadakar da matasansu akan illar aikata miyagun ayyuka.
Dubban Fulani ne suka taru a garin Kainji dake jihar Neja inda shugabannin Fulanin suka yi Allah wadai da yadda wasu matasan ke aikata wasu ayyukan asha a tsakanin al'umma. Shugabannin sun ce al'amarin na zubar da kimar Fulani a idanun duniya.
Alhaji Muhammad Kirwa Ardon Zuru kuma shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya yace kawo yanzu sun samu kawar da zaman tankiya dake tsakaninsu da Yarbawa dake kudu maso yammacin Najeriya.
Can baya dai kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta baiwa Fulani wa'adin ficewa daga yankin.
Alhaji Kirwa yace tafiyar da suka yi ta sa matsalolin da suke fuskanta a kasashen Yarbawa da na Igbo sun ragu matuka. Nufin Fulani ne su tabbatar duk kabilar dake Najeriya ta zama tana da fahimta akan Fulani saboda dabi'ar Bafillace daban take.
A babban taron Fulanin sun cimma wata matsaya game da babbar kasuwar dabbobi ta kasa da kasa dake garin Wawa a jihar Kwara. Inji Alhaji Kirwa sun dakatar da kasuwar har zuwa wani lokaci saboda su samu natsuwar mutanensu.
Yanzu Fulanin suna shirin ganawa da gwamnatin jihar Neja tare da majalisar dokoki dangane da dokar da majalisar ke son kafawa wadda zata haramtawa Fulani daukan makamai da suka hada da sanduna da adduna da bindigogi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5