Shugabannin ECOWAS Sun Kammala Taronsu A Abuja

ECOWAS

Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma, wato ECOWAS, sun kammala taron kwanaki biyu a babban birnin tarraiyar Najeriya, Abuja. inda suka koka da tabarbarewar harkar tsaro da ke addabar yankin tare da tattauna samar da sabbin hanyoyin dakilesu.

Wanan taron shi ne na 56 da shugabanin ECOWAS za su yi domin tattauna hanyoyin dakile tabarbarewar tsaro da ke addabar yankin, kamar yadda shugaba Mohammadu Buhari ya yi bayani, inda ya ce ta'addanci shine kan gaba wajen yi wa yankin barazana, wanda ya ke kawo rashin tsaro da zaman lafiyar al'ummar wannan yanki.

Saboda haka dole ne a hada karfi da karfe domin shawo kansa kuma babu abin da zai kawo ci gaba a wannan aikin da ya wuce hada kawunan mu - inji Buhari.

A nashi jawabin, shugaban kungiyar ECOWAS, kuma shugaban kasar Nijar, Mohammadu Yusuf, ya amince da bayanan da Shugaba Mohammadu Buhari ya yi a lokacin taron.

Shima shugaban kungiyar Hadin Kan Kasashen Afrika ta Yamma, Jean Claude Brou, ya ba kasashen karfin gwiwa ne, inda yayi bayanin cewa duk da barazanar rashin tsaron da yankin ke fuskanta, kuma ya ke fama da shi, ana samun ci gaba a fanin tattalin arzikin yankin, wanda ya kai kashi 3.3 a wanan shekara mai karewa, kuma kasashe bakwai daga cikin kasashen 15 na yankin sun samu karin kashi 6 cikin dari na tattalin arzikinsu.

Amma ga kwararre a fanin kimiyar tsaro na kasa da kasa, Kabir Adamu, ya ce idan yankin na so ya samu ci gaba a yaki da ta'addanci, sai ya yi hobbasa wajen aiwatar da shawarwarin taron da suka yi a Ougadougu a kasar Burkina Faso, wanda ya kunshi kara wa jami'an soji da na hadin gwiwa karfi, tare da tabbatar da hadin kai wajen tattara bayanan sirri tsakanin kasashen saboda a samu ci gaba a wajen yaki da yan ta'adda.

Daga cikin shugabanin da suka halarci taron akwai shugaban Bankin Ci gaban Afrika, Akinwunmi Adeshina da wakilin shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Mohammed Ibn Chambas. Akwai shugabanin Nijar, Togo, Burkina Faso, Guinea da kuma Gambia. Sauran shugabanin kasashen sun aika da wakilansu ne.

Ga karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin ECOWAS Sun Kammala Taronsu A Abuja