Kasar Taiwan ta bayyana cewa shugaban kasar ta Ma Yin-Jeou zaiyi ganawar garin da garin da shugaban kasar China Xi Jiangping.Kuma ranar lahadin nan mai zuwa ne za’a yi wannan ganawar, wanda rabon da ganin shugabannin kasashen biyu sun ganatun a shekarar 1949.
Mai magana da yawun shugaba Ma, Yace za’a yi ganawar ce a kasar Singapore, kuma ba za’a sa wa ko wata yarjejeniya hannu ba, amma yace shugabanninzasu gana ne da zummar karfafa dangataka tsakanin su , kana aci gaba tsayawa a halin da ake ciki.
A bangare guda kuma mahukuntar kasar China sun gasganta wannan batun ganawar .
Anan Amurka ko mai magana da yawun Fadar White House John Earnest ya shaidawa manema labarai cewa babban abinda Amurka ke bukata game da wannan ganawar shine a samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasashen biyu, kuma Amurka a shirye take ta ga hakan ya cimma nasara.