Shugabannin Amurka da Israila Sun Zanta Ta Wayar Tarho Jiya Lahadi

Sabon Shugaban Amurka Donald Trump da Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu

Jiya Lahadi Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bude taron majalisar ministocinsa na mako-mako ta kara kusantar babbar kawarta Amurka, da sabon shugabanta.

Shugabannin biyu sun zanta ta wayar tarho, har aka ji Trump yana cewa "tattaunawar ta yi kyau sosai."Bai tabo batun Isra'ila ta kaurarda helkwatar kasar daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus ba.

Daga bisani Firayim Minista Netanyahu ya ce shugaba Trump ya mika masa goron gayyata zuwa Washington cikin watan gobe.

Kamin shugabannin su yi magana, Fadar White House ta ce "yanzu ne ma ta fara batun tattaunawa kan kauradda fadar Isra'ilar", mataki da Trump yace yana goyon baya.

"Muna taya shugaba Trump murnar kama aiki” Netanyahu ya fada tun farko a jiya Lahadi. "Ina farin ciki ko godiya ga abokantakarsa mai zurfi da Isra'ila, da kuma kudurinsa na zahiri na yaki da 'yan ta'addan da ke ikirarin Islama da karfi sosai."

Fadin hakan ana ganin tamkar shagube ne ga tsohon abokin hamayyarsa a Fadar White House watau shugaba Obama, wanda yaki amfani da kalamar "Radical Islamic terrorism" da turanci.