Shugabannin Addinai A Kaduna Na Takaddama Kan Batun Satar Mutane

shugabannin Addinai

Yawan hare-hare da sace mutane a jahar Kaduna ya tsananta cecekuce tsanin shugabannin addinai ta yadda harma majalisar limamai da malamai ta jahar Kaduna ke Allah wadarai da al'amarin.

Sakataren majalisar limamai da malamai na jihar Kaduna, Malam Yusuf Yukub Arrigasiyyu ne ya yi wa manema labarai bayani kan taron gaggawa da majalisar ta kira a garin Kaduna.

Arrigasiyyu ya ce kalaman shugaban kungiyar kiristocin za su iya haddasa rashin fahimta tsakanin mabiya addinai a jihar Kaduna idan ba a dauki mataki ba.

Shi ma limamin Unguwan Rimi, Imam Musa Tanimu, wanda ya yi magana da yawun limamai kuma ya nuna damuwa ya na mai cewa an kama Musulmi da limamai da dama amma basu taba jingina wannan matsala a kan addini ba.

To sai dai shugaban kungiyar kiristoci ta jihar Kaduna Reveran Joseph John Hayap ya ce daukar nauyin kungiyar limamai aka yi shi ya sa su ka jirkita ma'anar bayanin da ya yi game da yawan sace-sace a jihar Kaduna.

Rev. ya ce ba inda ya ce kiristoci kawai ake sacewa a jawabin shi amma dai tun da shi shugaba ne dole ya kare muradin mabiyan shi saboda ya ce har gida ake bi ana sace kiristoci a Kaduna ba sai sun fita kan hanya ba.

Duk da bayanan kokarin kawo karshen sace-sacen mutane da gwamnatoci ke yi a arewachin Nigeriya dai har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin dauki dai-dai a wasu sassan wannan kasa.

Ga dai wakilin Muryar Amurka, daga Kaduna, a Najeriya. Isah Lawal Ikara:

Your browser doesn’t support HTML5

SATAR MUTANE YA HADDASA RIKICI A KADUNA