Dr Mohammed Sani Ayagi wanda ya jagorancin sallar idi a masallacin idi na harabar tsohuwar Jamia’ar Bayero dake nan Kano.
Baya ga tambihi akan bukatar al’ummar musulmi suyi riko da darussan da suka koya a watan ramadana,
Malamin ya hori ‘yan Siyasa da su rika la’akari da matsalar al’umma a lokacin da suke fafutikar cimma muradun su na kama madafun iko, Ga Kuma abinda malamin ke cewa.
‘’Harkar siyasar nan ban tun yau take muna illa ba, al’ummar musulmi harkar siyasa ta dade tana yi musu illa, kuma duk abinda ke ruruta wannan shine son rai da son zuciya musammam kasashen Musulmai na gabas ta tsakiya yadda muke ganin Baraka ako da yaushe suna bullowa dole ne mu dauke abinda ke kawo son zuciya mu dauki abinda ALLAH yake so.’’
Shima a jawaban su na Sallah Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Mallam Muhammedu Sanusi na biyu sun nanata muhimmacin hadin kai tsakanin Al’ummomi daba-daban dake zaune a cikin jihar ta Kano .
Ga Mamud Ibrahim Kwari da Karin bayani 3’26
Your browser doesn’t support HTML5