Shugabanni a jihar Niger Nigeria sunyi anfani da bukukuwar karamar Salla wajen janyo hankalin jama’a akan muhimmacin zaman lafiya da kuma hadin kan kasa, al’amaerin dake nuna suna mayar da martini ne akan masu kiraye-kirayen ganin an raba Najeriya, domin kafa kasar Biafra a can yankin yan kabilar Igbo.
WASHINGTON DC —
Gwamnan jihar Niger Alhaji Abubakar Sani Bello a cikin sakon sa na Sallah cewa yayi.
‘’Ina fata ALLAH ya karbi ibadar mu duka,ALLAH ya bamu zaman lafiya a jihar Niger da Nigeria ga baki daya, Kuma ALLAH ya gwada muna Ramadan na badi’’.
Suma sarakunan gargajiya na jihar Niger ba suyi kasa a gwiwa ba wajen bayyana wa al’ummomin su muhimmacin hadin kan Nigeria.
Kamar yadda mai martaba sarkin sudan na Kontagora Alhaji Saidu Namaska ya bayyana a cikin jawabin sa.
Ga wakilin sashen Hausa Mustafa Nasir Batsari da Karin bayani.1’51
Your browser doesn’t support HTML5