‘’Kuma kunji sakon da aka kawo nan lallai sojoji suna kula da rikon kasa, to ya kamata ko wane lokaci a rika yi musu addu’a, domin kasar mu ta zauna lafiya domin mu samu kwanciyar hankali’’
Shima Magajin garin birnin konni yabi wannan sahu inda yayi fata ga jamaa da suyi anfani da wannan damar ta salla domin suwa junan su gafara hakazalika tare da yin adduoi domin ALLAH ya dawwamar da zaman lafiya a cikin wannan kasar. Yaci gaba da bayanin cewa
‘’ALLAH ya kare kasar tamu kuma duk wani mai niyyar shairi zuwa ga kasar mu ko kuwa ga garin mu, ko kuma gidajen mu ALLAH ya tona masa asiri, ALLAH kar ka bashi iko,yadda muka taru nan akayi addu’a ALLAH ya tsare kasar tamu, ALLAH ya karbi addu’ar mu.’’
Amma shiko wakilin sarkin konni a nasa jawabin gargadi yayi wa jamaa, da su kiyaye da ibadar da suka yi domin kar su shiga wata masha’a su narke duka ladar da suka samu a lokacin wannan azumin watan ramadana .
Ga wakilin sashen Hausa Haruna Mamman Bako da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5