Shugabanci Nagari Ke Kawo Zaman Lafiya

Alhaji Aminu Waziri Tambuwal kakakin majalisar wakilan Najeriya

A firar da ya yi da Muryar Amurka kakakin majalisar wakilan Najeriya ya ce shugabanci nagari ke kawo zaman lafiya cikin kasa.
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya da wasu 'yan majalisar sun kawo ziyara Amurka inda kakakin ya bada wasu kasidu da suka hada da shugabanci da harkar tsaro a Cibiyar Hulda Kan Harkokin Waje Ta Amurka da Jami'ar John Hopkins.

Kakakin Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi fira da Murya Amurka inda ya tabo batutuwa da dama cikinsu har da cewa shugabanci nagari shi ne ke kawo zaman lafiya. Game da shugabanci kakakin ya ce cigaba da zaman lafiya basu yiwuwa idan shugabanni suka zama dodon bango waddanda suka manta da talakawan da suka zabesu. Ya ce yiwa mutanen da suka zabi mutum kunne shegu dole matsala ta taso. Najeriya dake cikin kasashe masu tasowa da take kuma jaraba dimokradiya nada matsalar shugabanci.

Dangane da rabuwar PDP gida biyu ya ce babban dalilin shi ne na rashin shugabanci nagari. Shugabannin sun ki su zauna su saurari mutane su bude damuwarsu su kuma maganceta su ne suka sa aka kaiga cecekucen da ake yi yanzu.An ki bin tsarin jam'iyya da ya ba kowa daman ya fadi abubuwan dake damunsa da korafe- korafensa a kuma daidaita a yi tafiya tare.

Shugabancin Najeriya yana neman gyara. Yana da matsaloli. Wajibi ne a duba a kuma gyara domin a samu cigaba.Dole a tabbatar cewa an samu shugabanci ingartacce ga al'umma. Hakika kasa bata cigaba da yin watsi da mutanen da suka zabi shugabannin.

Game da rikicin jam'iyyarsa ta PDP matsayinsa shi ne a warware matsalar. A daidaita kana a dawo a yi tafiya tare. Ya ce a majalisa 'yan bangarorin biyu suna ganisa a matsayin shugabansu don haka babu batun wane bangare shi yake. An tambayeshi baya goyon bayan gwamnasa wanda yake sabon bangaren jam'iyyar sai ya ce dangantakarsa da gwamnan daban ce da matsayinsa na shugaban majalisa. Game da ko zai tsaya takarar shugaban kasa sai ya ce idan lokaci ya yi bayan tuntubar mutane ya yi bayani.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabanci Nagari Ke Kawo Zaman Lafiya-