Shugabanci: Majalisar Dattawa Ta Sake Gaurewa Da Takaddama

  • Ibrahim Garba

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Yayin da Majalisar Dattawan Najeriya ke jiran sunayen Ministoci daga Fadar Shugaban kasa, Majalisar ta sake gaurewa da rigimar Shugabaci

Bayan dawowa daga hutu, zaman farko na Majalisar Dattawan Najeriya ya gaure da zafaffiyar muhawara wadda ke da nasaba da shugabancin Majalisar Dattawan. Gardama ta fara barkewa ne tsakanin Shugaban Majalisar Dattawan Abubakar Bukola Saraki da kuma Sanata Kabiru Marafan Gusau.

Wakiliyarmu a Majalisar Dattawan Madina Dauda ta ce hatsaniyar ta faru ne bayan da Shugaban Majalisar Dattawan ya yi jawabin maraba, inda Sanata David Umaru na APC daga jahar Naija ya nemi ya gabatar da kudurin nuna goyon baya ga Shugaban Majalisar saboda, a ta bakinsa, a samu natsuwa da kuma damar yi ma jama’a aiki, inda shi kuma Sanata Kabiru Marafan Gusau ya ce sam.

Bayan hatsaniyar, ‘yan’majalisa tamanin da uku sun kada kuri’ar amincewa da shugabancin Shugaban Majalisar. A halin da ake ciki kuma, da Madina ta tambayi mai magana da yawun Majalisar Dattawan Sanata Dino Melaye ko an sami wasika daga Fadar Shugaban kasa sai ya ce lallai sun sami wasiku daga Fadar Shugaban kasa. Akwai wasikar nada Babban Ciyaman na hukumar FRIS, da kuma ta nada babban manajan AMCON da kuma ta nada Mataimakin Babban Ciyaman na Hukumar Sadarwa Ta Kasa kuma daga gobe za su fara aiki a kansu. Ya ce daga yanzu zuwa dare sun a kyautata zaton za a samu sunayen Ministoci daga Fadar Shugaban kasar.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabanci: Majalisar Dattawa Ta Sake Gaurewa Da Takaddama - 2'18''