Amma jam’iyyar adawa tace zata kalubalanci zaben da aka yi shi ranar jiya Lahadi, inda suke zargin cike yana cike da magudi. Nasarar da Erdogan ya samu zata bashi damar tsallake ‘yan majalisu haka kuma zai iya nada Ministoci da alkalai da manyan jami’an gwamnati ba tare da amincewar majalisa ba. Yana kuma iya dakatar da majalisa
Shugaban kasa Erdogan ya yiwa magoya bayan sa dake ta sowa jawabi a yammacin jiya Lahadi bayan an rufe rumfunan zabe.
An dai bukaci masu kada kuri’a da su goyi bayan kuduri na sha takwas domin gyaran tsarin mulkin kasar wanda zai maye gurbin tsarin mulkin da ake dashi a yanzu. Kasashen duniya da dama sun soki tsarin.
Jam’iyyar adawa ta Turkiya tace zata kalubalanci zaben a kotu saboda sunaganin an yi magudi.