A ranar Asabar 25 ga watan Yuli Shugaban Tunisia Kais Saied ya nada Ministan cikin gidan kasar a matsayin sabon Firai Ministan da zai maye gurbin Elyes Fakhfakh, wanda ya yi murabus saboda zarge-zargen sabanin ra’ayi, a cewar fadar gwamnatin kasar.
Sabon Firai Minista Hichem Mechichi ya yi alkawarin daukar matakai akan bukace-bukacen harkokin zamantakewa da tattalin arziki da ke haddasa yawan zanga-zanga a kasar da ke arewacin nahiyar Afrika.
Mechichi, dan shekara 46, ya na da tsawon wata guda ya kafa gwamnatin da za ta samu nasara da rinjaye a kuri’ar kwarin gwiwa da majalisar dokokin za ta kada, ko kuma Shugaban zai soke majalisar dokokin ya sa a sake yin zabe.