Shugaban Kasar Somaliya Na Ziyarar Aiki a Eritiriya

  • Ibrahim Garba

Shugaba Mohammed Farmaajo

A wani al'amari mai kafa tarihi, yankin kuryar Afirka da ya hada da kasashen Habsha, da Eritiriya da Somaliya da Djibouti na dada samun kwanciyar hankalin da ya jima bai gani ba. Hasali ma a yanzu haka Shugaban kasar Somaliya na kasar Eritiriya wajen kara dankon zumunci.

Shugaban kasar Somalia Mohammed Abdullahi Farmajo ya fara ziyarar aiki a kasar Eritiriya ta kwanaki uku mai cike da tarihi, inda ya tattauna da takwaran aikinsa na kasar tun daga isowarsa jiya Asabar a birnin Asmara.

Ministan Yada Labarai na kasar ta Eritiriya ya sanar tun ranar Jumma'a cewa Shugaban kasar Eritiriya Isaias Afwerki ya gayyaci Shugaban na Somalia.

Kasashen biyu sun shafe shekaru 15 ba tare da wata huldar diflomasiyya ba.

Wannan ziyarar ta Farmajo ta faru ne bayan da Eritiriya da kasar Habasha, wadda su ka dade su na gaba da ita, su ka maido da huldar jakadanci, matakin da ya kawo karshen mayar da Eritiriya saniyar ware a yankin.