:
Jami’an gwamnatin Somalia sun ce shugaban kasar da PM duk suna nan lafiya, bayan wani hari da mayakan sakai na kungiyar al-Shabab suka kai kan fadar shugaban kasar a Mugadishu babban birnin kasar.
Shaidun gani da ido sun bada labarin jin karar fashe-fashe kuma an yi ta musayar wuta a ciki da kewayen fadar shugaban kasar, a yammacin jiya talata, lokcin da ‘yan binidga suka yi kokarin kutsawa cikin fadar shugaban kasa.
Haka kuma shaidun sun bada labarin cewa daga bisani a wajajen almuru fadan ya lafa.
A cikin sakonnin da ofishin shugaban kasar ya wallafa a dandalin twitter, yace an tarwatsa yunkurin kaiwa fadar shugaban kasar harin, sakamakon bajintar da sojojin kasar da masu aikin kiyaye zaman lafiya daga kungiyar hada kan kasashen Afirka suka nuna.
Shugaba Hassan Sheikh Mohamoud, ba ya cikin fadar lokacin da aka aka kai harin.
A halinda ake ciki kuma, MDD ta tura agajin abinci na gaggawa zuwa kasar Sudan ta kudu inda tace akwai alamun kasar zata fada cikin bala’in ‘yunwa.