Shugaban Rasha Ya Ba da Umurnin Tsagaita Wuta A Syria

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Jiya Litinin shugaban kasar Rasha wanda yake goyon bayan gwamnatin Assad ya ba da umurnin tsagaita wuta a yakin kasar Syria duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudurin yin hakan tun ranar Asabar

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bada umarni jiya Litinin na tsagaita wuta na tsawon sa'o'i biyar a kullum daga hare-haren da Moscow ke kaiwa ta sama a kan 'yan tawayen Syria, bisa dalilan jinkai, domin ba farin kaya damar kauracewa wuraren da ake tashin hankali kusa da birnin Damascus.

Ministan tsaron kasar Rasha, Sergei Shoigu, yace daga yau Talata Rasha zata rika tsagaita wuta daga karfe tara na safe zuwa biyu na rana agogon kasar, “da nufin kare fararen kaya,”. Yace an bude wata hanya ta musamman ta jinkai, domin farin kaya su fice daga birnin, ya kuma ce hukumomin kasar Syria suna rarraba takardu da cikakkun bayanan hanyoyin ficewar.

Putin ya bada umarnin ne kwana biyu bayan fara aiki da shirin tsagaita wutar kwanaki talatin da dukkan wakilan Kwamitin Sulhun MDD suka bukaci a aiwatar a fadin kasar ta Syria. An ci gaba da fada a Ghouta dake bangaren gabashin Damascus,babban birnin kasar, inda aka kashe sama da mutane talatin jiya litinin, bisa ga cewar ‘yan gwaggwarmaya, yayinda aka ci gaba da kai hare hare ta sama da kuma tada boma bomai.