A yayin taron da aka fara yau kuma za a kammala zuwa gobe, tawagar Jamhuriyar Nijar a karkashin jagorancin shugaban kasa Issoufou Mahamdou zata yi kokarin fadakar da masu hannun da shuni akan tsarin shirin kasar mai lakanin PEDES.
Shirin na kunshe da ayyukan bunkasa tattalin arziki da inganta hanyoyin jin dadin rayuwar al'umma a cewar Ministar fasali Aishatu Bulama. Ta ce cikin tsarinsu sun saka sefa miliyan dubu goma sha biyar.
Daga cikin kudin, gwamnati zata sa fiye da miliyan dubu tara a matsayin jarin gudanar da aiki cikin kasar. Saboda haka, zuwansu Paris ba zuwan yin bara ba ne. Tallafin ciko suke bukata domin su aiwatar da ayyukansu.
Suna da burin sake gina karkara da tallafawa manoma da makiyaya da masu sarafa kayan gona. Za su kai lantarki a garuruwa da kauyuka dubu da yin hanyoyi da kuma taimakawa mata da yaran karkara, musamman yaran da ba su taba shiga makarantar boko ba.
Karfafa ayyukan kamfanoni masu zaman kansu na cikin abubuwan da gwamnatin Nijar zata mayar da hankali akai a wurin tattaunawar ta birnin Paris. Aisha Bulama ta kara da cewa, muddin ana son kasa ta ci gaba ta fannin tattalin arziki, dole ne a taimakawa kamfanoni masu zaman kansu.
Yin hakan zai bukaci sharewa masu saka jari daga waje fagen gudanar da harkokinsu ba tare da kawo masu cikas ba. Masu bin diddikin harkokin kasar ta Nijar na da shakku akan lamarin.
Malam Lawali Abubakar shine mai shugabancin wata kungiya da ke fafutukar kare dimukuradiyya, cewa yayi, mutane na ganin shugaban kasa zai dawo daga Paris da kudade masu yawa, amma hakan ba zai yiwu ba saboda an ayyana kasar ta Nijar daga cikin kasashen da basu da dimukuradiyya.
Yace kowa ya sani yau a Nijar, talaka shine yake wahala saboda a ko ina mutum ya shiga a kasar ana zacen cin hanci da rashawa ne da wasu abubuwan masu yawa da suke sa shakku akan kasar ta Nijar. A shekarun baya dai maganar yakar ayyukan ta'addanci ne ya lakume yawancin kudaden kasafin kudin kasar.
Ga rahoton cikakken rahoron Sule Mumuni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5