Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kakkausar murya game da sabon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a wasu kauyukan jihar Kaduna.
Shugaban ya nuna bakin ciki akan harin da ‘yan bindiga suka kai a garin Igabi da karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Sanarwar da ta fito daga kakakin Shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, shugaba Buhari ya aike da gargadi mai karfi ga ‘yan ta’addan.
Mallam Garba Shehu ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari ba zata yi kasa a gwiwa ba na ganin an kawar da ta’addanci a Najeriya baki daya. Kuma Shugaban ya bada tabbaci ga al’ummar jihar Kaduna cewa, gwamnatin sa zata ci gaba da yaki da ta’addanci.
Almustapha Liman, wani mai sharhi akan al’amurran da suka shafi tsaro a Najeriya, ya ce, ya kamata gwamnati su sake damarar yaki da ta’addanci.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5