Mai martaba Lamidon Adamawa, Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, ya yi wa shugaban kasa Muhammad Buhari kyakyawar karba a fadarsa yayin ziyarar aiki na kwana guda a Yola, don bude taro kan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin jihar ta shirya.
Lamidon Adamawan dai ya mika kukar al’ummar jihar kan batutuwa da suka hada da batun aikin madatsar ruwan Chouchi da aka dakatar yau fiye da shekaru 17, da batun maida jami’ar kimiyya da fasaha ta Modibbo Adama ta koma kamar sauran jami’o’i da kuma daga darajar babban asibitin gwamnatin tarayya dake Yola, wato FMC Yola, zuwa asibitin koyarwa, batun da ko shugaban Najeriya yace za’a duba.
Da yake tarbar shugaban Najeriya a wajen bude taron, gwamnan jihar Adamawa, Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, ya gode bisa daukin da shugaban kasa ke baiwa gwamnoni musamman ta wajen biyan albashi.
To sai dai kuma fa da alamun ziyarar ta shugaban kasar ta bar baya da kura inda masu kananan sana’o’i suka koka game da rusa musu rumfuna da aka yi, da sunan zuwan shugaban kasa.
To ko me 'yan siyasa ke cewa game da zuwan shugaban kasar? Hon.Abdullahi Prembe tsohon kwamishinan yada labarai ne a jihar ya koka da yadda aka maida su ‘yan jam’iyyar PDP saniyar ware alhali kuwa a lokacinsu sun ba ‘yan adawa mukamai, in ji shi.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5