Shugaba Buhari Ya Kira Shugabannin Binuwai Su Shawo Kan Al'ummarsu Domin Zaman Lafiya

Buhari Tare Da Gwamnan Binuwai

Biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Fulani da wasu al'ummomin jihar Binuwai wanda ya lakume rayuka da dama ya kuma raba wasu da muhallansu, Shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa al'ummar jihar jaje tare da kiran a hada kai a samu zaman lafiya

Yayinda ya kai ziyarar yini daya zuwa jihar Binuwai, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihar da su yi kokarin shawo kan al'ummarsu domin a samu zaman lafiya a jihar.

A jawabinsa Shugaban ya bukaci shugabannin jihar ta Binuwai da su hada kai da jami'an tsaro domin a tabbatar da zaman lafiya. Inji shugaban hakki ne da ya rataya akansu su dinga ganawa da mutanensu lokaci lokaci tare da basu shawarar zama lafiya.. Injishi "duk muna bukatar juna a Najeriya".

A nashi jawabin gwamnan jihar Samuel Ortom ya ce baicin rayuka da aka yi asararsu, akwai mutane fiye da dubu 170 da suke gudun hijira inda kashi 60 cikinsu yara ne da yanzu basa zuwa makaranta.

A cewar gwamnan wani shiri na musamman da suka yiwa 'yan ta'addan jihar sun samu karbar makamai fiye da dari bakwai da suka lalata. Gwamnan ya ce gwamnatinsa bata goyon bayan ayyukan ta'addanci saboda haka basu ajiye wani dan ta'adda ba.

Shi ma basaraken gargajiya na kablar Tiv Farfesa John Ayase ya bukaci gwamnatin tarayya ta yiwa harkar tsaro garambawul ta yadda sarakunan gargajiya zasu taka irin tasu rawar. Ya kuma kira gwamnatin tarayyan ta magance kwararowar hamada wadda a ganinsa na cikin abubuwan dake taimakawa cikicin. Ya kuma nemi a magance matsalar munanan hanyoyin jihar.

Kwamandan kungiyar dake sa ido a harkokin tsaron jihar Alhaji Aliyu Tishako ya yi jawabi a wurin taron yana jaddada alfanun zaman lafiya. Haka ma shugaban Miyetti Allah reshen jihar Alhaji Haruna ya yi tare da fatan za'a kawo karshen tashin hankalin.

.Ga Zainab Babaji da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Kasa Ya Kira Shugabannin Binuwai Su Shawo Kan Al'ummarsu Domin Zaman Lafiya - 4' 06"