Shugaba Muhammad Buhari ya kaddamar da kwamiti mai mutane 30 wanda zai yi nazari da yin tsari na sabon tsarin albashi na ma'aikacin Najeriya mafi kankanta daga Naira 18,000 zuwa wani kaso da ya fi hakan.
A lokacin da shugaban yake kaddamar da kwamitin ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta bi sawun sauran kasashe na duniya inda za ta inganta albashin ma'aikaci saboda mahimmancinsa wajen ci gaba da kuma daukaka kasar da yake yiwa aiki.
Ganin yadda abubuwa suka canza albashi mafi kankanci yanzu ya tsufa dole ne a kawo wani sabo da zai zo daidai da rayuwar yau.
Cikin gwamnonin da suka halarci bikin akwai gwamnan Kebbi Atiku Bagudu wanda ya yi tsokaci akan abun da shugaban ya yi yau. Ya ce kwamitin ya kunshi mutane daga sassa daban daban. Akwai mutanen gwamnatin tarayya, akwai na jihohi, akwai na 'yan kasuwa da kungiyoyin kwadago da kamfanoni dake zaman kansu domin a tsaya a yi abun da hankali zai yi da zai ciyar da Najeriya gaba.
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya Ayuba Wabba ya ce sun yabawa shugaban kasa da ya kafa kwamitin. Yace a shirye suke su yi sulhu da shugaban kasa su kuma yi aiki da duk shawarar da kwamitin din ya tsayar.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5