Shugaban Najeriya Ya Dakatar Da Kungiyar Super Eagles

Goodluck Jonathan ya bayar da umurnin dakatar da kungiyar daga shiga duk wata gasar kwallon kafa har na tsawon shekaru biyu.

Shugaban Najeriya ya dakatar da kungiyar kwallon kafa ta kasar, Super eagles, daga shiga duk wata gasa ta kasa da kasa har na tsawon shekaru biyu masu zuwa, a bayan da kungiyar ta kasa tabuka komai, aka kuma fitar da ita tun zagayen farko na gasar cin kofin Kwallon Kafar Duniya a Afirka ta Kudu.

Wani kakakin shugaba Goodluck Jonathan mai suna Ima Niboro, ya fada laraba cewa an dakatar da kungiyar ta Super eagles daga shiga duk wata gasa ce domin tabbatar da cewa "ba a sake nanata abin kunyar da ta yi lokacin Gasar Cin Kofin Duniya a Afirka ta Kudu ba." Ima ya ce Najeriya zata dauki wannan lokaci wajen sake yin garambawul ga harkokin kwallon kafa a kasar.

Magoya bayan Super Eagles

An yi fatali da 'yan Super eagles daga gasar a bayan da suka kammala zagayen farko da maki daya tak, a sanadin kunnen-dokin da suka yi da Koriya ta Kudu. Kasar Ajantina ta doke su ad ci daya da babu, kasar Girka kuma ta doke su da ci biyu da daya.

Shugaban Kwamitin Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya a Najeriya, Rotimi Amechi, ya ce janye 'yan Super Eagles daga duk wani wasa zai ba kasar damar zama da samo hanyar magance irin wannan lamarin. Ya ce janye kungiyar daga duk wani wasa bai saba ma dokokin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, wadanda suka haramtawa gwamnatoci yin katsalanda a harkokin kwallon kafa ba.