Wata sanarwa da mai baiwa shugaba kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar a yau Talata ta nuna cewa, Buhari ya nemi tsawaita hutunsa ne bayan wasu gwaje-gwaje da aka yi masa wadanda suka nuna bukatar hakan.
Sai dai sanarwar ta nuna cewa kada ‘yan Najeriya su damu domin ya na cikin koshin lafiya, ba tare ta ambaci ranar da shugaba Buhari mai shekaru 74 zai koma Najeriya ba.
Shugaban na Najeriya, wacce ita ce kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika, ya bar kasar tun ranar 19 ga watan Janairu ba a kuma ji duriyarsa ba, sai dai hotunansa da su ke bayyana.
Tun a ranar 5 ga watan Fabrairu ya kamata Buhari ya koma kasar, amma ofishinsa ya fitar da sanarwar cewa likitoci sun bukaci da ya dakata ya ga sakamakon binciken da aka mai.
Makusanta shugaban har ya zuwa yanzu ba su fadi takamaiman abin da ke damun shugaba Buhari ba, lamarin da ya haifar da rade-radin cewa ya na cikin mawuyacin hali
Sai dai duk da haka, an kawar da fargabar barin kujerarsa ba tare da kowa a kai ba, domin tun kafin ya tafi ya mikawa mataimakinsa Yemi Osinbajo ragamar mulkin kasar.
Najeriya ta taba kusantar rudani a kundin tsarin mulkinta a shekarar 2009 a lokacin marigayi shugaba Umaru Musa ‘Yar adua ya tafi neman magani ba tare da ya nada kowa a mukaminsa ba.
Hakan ya sa a lokacin Majalisar Dattawan kasar ta mikawa mataimakinsa Goodluck Jonathan ragamar mulkin kasar ta Najeriya.