Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya gana cikin siri da manyan hafsoshin sojojin kasar a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja.
Sun kwashe sa’o’i hudu suna ganawa amma daga karshe ba’a bayyanawa ‘yan jarida makasudin taron ba.
To sai dai masana irinsu Farfesa Muhammad Tukur Baba na ganin ganawar na da tasiri ga sha’anin tsaron kasa. Yana mai cewa wajibi ne ma shugaban ya dinga ganawa da jami’an tsaro kowane mako saboda irin yanayin da kasar ke ciki.
Shi kuwa Aliko El-Rashid Haroun, wani tsohon hafsa a rundunar tsaron Najeriya, cewa yake akwai matsaloli da dama kamar ‘yan IPOB masu rajin neman kafa kasar Biafra dake bukatar a rinka maida hankali a kansu, ga kuma matsalar masu garkuwa da mutane.
Shi ma Air Commodore Baba Gamawa yace irin wannan ganawar ta shugabannin ma’aikatun tsaro ba wani sabon abu ba ne. A cewarsa, daga lokaci zuwa lokaci ya kamata shugaban kasa ya dinga zama da jagororin tsaro don a rinka nazarin ci gaban da aka samu da kuma matsalolin da ake fuskanta.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5