Shugaban Najeriya da Gwamnoni Sun Dauki Matakan Bunkasa Tattalin Arziki

Gwamnan Jigawa Mohammad Badaru Abubakar

Gwamnatin Shugaba Buhari tare da gwamnonin jihohi sun kafa wani zaure na tsawon makonni shida inda masu saka jari da kafa masana'antu akan noma, sufuri, da makamashi zasu hadu su tsara ayyuka 240 da aka kayyade.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da gwamnoni da manyan 'yan kasuwa masu saka jari a fannoni daban daban sun kaddamar da wani zaure da zai zama tubalin bude wata babbar kasuwa da zata biya bukatun duk masu neman kafa masana'antu.

Kasuwar zata ci ne a cikin sati shida. Zata biya bukatun duk masu neman kafa masana'antu, musamman a fannin noma.

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar yana cikin gwamnonin da suka halarci taron tare da shugaban kasa, shi ne ya tattauna da manema labaru akan wannan gagarumin shirin na gwamnati.

A cewarsa daya daga cikin hanyoyin bunkasa tattalin arziki ita ce a kirkirii zauve guda daya inda duk abun da ake nema na gwamnati yana cikin zauren. 'Yan kasu da wadanda zasu saka jari sun samu duk abubuwan da suke nema a zaure daya dangane da masana'antun da zasu kafa. A sabon shirin an dauki noma da sufuri da inganta masana'antu da inganta wuta da makamashi.

Zauren na tsawon makonni shida zai kula da abubuwa ko ayyuka 240. Komi mutum yake son ya yi a zauren zai samu abubuwan da yake bukata ya cimma burinsa. A zauren ne zai hadu da jami'an gwamnati ba sai ya bisu zuwa ma'aikatarsu daban daban ba. Cikin makonni shidan ne za'a gama tsara ayyuka 240 din.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Najeriya da Gwamnonin Sun Dauki Matakan Bunkasa Tattalin Arziki - 4' 05"