Tinubu Ya Tattauna Da Sarki Charles III A Taron COP28

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Sarki Charles III

A wani yunkuri na sauya fasalin makamashi mai tsafta a duniya da kuma magance matsalar sauyin yanayi, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya halarci taron COP28 na yanayi a Dubai na wannan shekara.

Taron wanda zai gudana daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba, ya samu halartar shugabanni daga kowane sassa na fadin duniya, hamshakan attajirai, da masu rajin kare sauyin yanayi daga kasashe kusan 200.

Halartar taron da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi, ya ba shi damar muhimmiyar ganawa da Sarki Charles na Ingila.

Wannan huldar diflomasiyya tana jaddada kokarin hadin gwiwa da ake bukata a matakin kasa da kasa don yaki da sauyin yanayi.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis ya bayyana cewa ya gana da Sarki Charles na kasar Ingila da nufin karfafa alakar Najeriya da kasar Birtaniya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafin X(twitter) gabanin taron kolin na COP28 da zai gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

"Na yi ganawa mai amfani da Mai Martaba, Sarki Charles III na Ingila wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar kasa-da-kasa ta Commonwealth, kuma mai kishin sauyin yanayi," Shugaba Tinubu ya rubuta.

"Ganawar ta kasance wani muhimmin mataki na karfafa dangantakar dake tsakanin Najeriya da Birtaniya."

Shugaba Tinubu ya bayyana kyakkyawan fata game da kokarin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Birtaniya, yana mai jaddada tasiri mai kyau da wadannan tsare-tsare na hadin gwiwa za su iya yi kan makoma da nasarar duniya baki daya.

Wannan shine karo na 28 na taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka fi sani da COP28 wanda yake gubana a hadaddiyar daular larabawa (UAE) a garin Dubai.

Taron dai zai kasance wata marhala don samar wa duniya mafita da sabbin hanyoyin magance matsalar gurbatar yanayi, da kuma nazarikan ci gaban da aka samu tun lokacin da aka amince da yarjejeniyar Paris.

Hannun jari na farko na Duniya (GST) ne zai ba da cikakkiyar kimanta ci gaban da aka samu tun lokacin da aka amince da yarjejeniyar ta Paris.

Hakan zai taimaka wajen daidaita kokarin da ake yi kan ayyukan sauyin yanayi, gami da matakan da ya kamata a dauka domin cike gibin da ake samu.