Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya ce zai mutunta hukuncin kotu na soke maido da Majalisar Dokoki da ya yi.
Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya ce zai mutunta hukuncin kotu na soke maido da Majalisar Dokoki da ya yi.
A wani bayanin da ya yi jiya Laraba, Shugaban ya ce zai nemi tattaunawa da bangarorin siyasa da na dokoki, da niyyar kawo karshen zaman dardar din da ya biyo bayan wannan takaddamar.
A makon jiya, Mr. Morsi ya bayar da umurnin maido da Majalisar, wadda ‘yan kishin Islama ke da rinjaye ciki, wadda gwamnatin mulkin sojan kasar ta rusa a watan jiya, bayan da kotun kolin kasar ta gano cewa an yi kuskure a tsarin zaben Majalisar.
Majalisar Wakilan kasar ta yi biris da umurnin sojojin kasar da kuma Kotun Kolin, ta yi wani dan takaitaccen zama ranar Talata.