A karon farko, Shugaban Majalisar Dokokin Janhuriyar Nijar Malam Hamma Ahmadu ya bayyana dalilan da su ka sa ya ke gudun hijira a wata hirar da ya yi da manema labarai a kasar Faransa. Kuma jama’a sun shiga bayyana ra’ayoyinsu.
Hamma Ahmadu, wanda ake zargi da taka rawa cikin wata badakkarar safarar jariari daga Nijeriya, ya ki gurfana a gaban kotu don kare kansa kamar yadda aka bukaci ya yi. Ya ce ya gudu ne saboda an yi niyyar a hallaka shi ta amfani da gubar da aka taho da ita daga kasar Libiya, wadda yaki ya daidaita a yayin yinkurin hallaka marigayi Shugaba Mu’ammar Gaddafi.
Tuni wasu na hannun damar Hamma Ahmadu su ka gaskata abin da ya fada saboda, a cewarsu, dattijo ne sosai, don haka shi bay a karya. Honorabul Sale Hassan Ahmadu Mataimakin Shugaban jam’iyyar Lumana Afirka ta su Mallam Hamma Ahmadu ya ce Hamma Ahmadu na da cikakken hujjoji dangane da zargin da ya yi na shirin hallaka shi. To amma su kuma bangaren masu rinjaye na Majalisar Dokokin Janhuriyar Nijar din kuma sun kira manema labarai, inda su ka yi watsi da zargin na Hamma Ahmadu. Honorabul Zakari Ummaru Dan Majalisar Dokoki karkashin PNDS-Tarayya y ace addu’a ce ta ‘yan Nijar da Allah ya amsa saboda, in ji shi, maguwar niyyar da ya yi wa Shugaba Muhammadu Issouhu. Wakilin Muryar Amurka da ya turo wannan rahoton, Abdullahi Mammane Ahmadu y a ce tuni sauran mutanen da ake zargi da hannu a fataucin jariran ke tsare a gidajen yari.
Your browser doesn’t support HTML5