Shugaban Laberiya Geoge Weah Ya Taka Ledar Minti 79

Shugaban kasar Liberia George Weah, ya bugawa kasarsa wasan kwallon kafa a ranar Talata 10/9/2018 yana da shekaru 52, Weah, shine dan kwallon Afirka na farko da ya lashe Kyautar gwarzon dan wasan kwallon kwallon kafa ta duniya FIFA, ya fafata wasanne har na tsawon mintuna 79 a wasan da Najeriya ta yi nasara da ci 2-1 a Monrovia.

Kasar Laberiya ta shirya wannan wasan na sada zumunci don janye riga mai lamba 14, wadda Weah yake sawa a yayin da yake taka leda.

Ku Duba Wannan Ma Kungiyar Tottenham Zata Sabubunta Kwagilarta Da Vertonghen

Najeriya ta zuba ‘yan kwallo sosai, ciki har da Wilfred Ndidi na Leicester da dan wasan tsakiya Peter Etebo na Stoke City da Ndidi, Kelechi Iheanacho, wanda suka zo a matsayin canji.

Weah, Tsohon dan wasan AC Milan, da Monaco, Paris St-Germain da Chelsea da kuma Manchester city, ya ajiye takalman wasansa tun shekaru 16 baya, lamarin da ya ba magoya bayan kasar mamaki ganin yadda ya buga wasan da Najeriya, ba tare da wata matsala ba har na tsawon mintuna 79.

An rantsaer da George Weah, a matsayin shugaban kasar laberiya a watan 2018 Janairu.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kasar Laberiya Geoge Weah Ya Takawa Kasar Sa Leda