Shugaban Kwamitin Riko Na PDP Ya Mayarda Martani Kan Zaben Rivers

Taron kwamitin riko na PDP a karkashin Sanata Ahmadu Makarfi

Kwamitin riko na PDP a taronsu da suka yi a Abuja sun ce da jam'iyyarsu ce ta lashe duk kujerun 'yan majalisar tarayya inda ba abokan hamayyarsu sun kawo masu cikas ba.

Shugaban kwamitin rikon Satana Ahmed Makarfi shi ya mayarda martani kan nasarar da PDP ta samu a zaben da aka yi a jihar Rivers.

Yace jihar Rivers ta PDP ce amma gwamnatin APC dake tarayya ta hada baki da jami'an tsaro ta murde zaben.

Dangane da fille kan DSP Alkali Muhammad da hadiminsa da 'yan bangan siyasa suka yi a jihar, Makarfi ya dora alhakin kan APC wadda yace ita ta ingiza jami'an tsaro kutsa inda bai kamata su kutsa ba da yin aikin da ba nasu ba ne.

Abdul Ningi sakataren shirye-shirye na kwamitin yace ya je Rivers inda jami'an tsaro suka hana ma'aikatan hukumar zabe ta INEC bayyana sakamakon zabe sai da suka ga mutanen Rivers sun taso da bala'i kana suka bari aka bayyana zabukan da aka ci. Ningi yace ya ji ciwon jami'in dansandan da aka kashe saboda cin zabe na Allah ne.

Amma APC ta bakin sakatarenta na kasa Mai Mala Buni tace korafin da PDP keyi illar rasa madafin iko ne bayan tayi mulki na shekaru goma sha shida.

Kawo yanzu dai rundunar 'yansandan Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda tayi watsi da zargin kutuntawa INEC kana tace ta kwafa kwamitin binciken kashe jami'anta da aka yi.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kwamitin Riko Na PDP Ya Mayarda Martani Kan Zaben Rivers - 2' 33"