Shugaban Kungiyoyin Fararen Hula Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasar Nijar Ta 2021

Nouhou Arzika shugaban kungiyoyin fararen hula na Nijar

Nouhou Arzika dake shugabancin kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar ya sha alwashin kalubalantar 'yan siyasa a zaben shekarar 2021 kuma yace shi ne zai ci zaben saboda 'yansiyasa sun kaucewa hanyar ciyar da kasar gaba

Nouhou Arzika ya zargi 'yan siyasar Nijar da nuna kasawa a harkokin mulkin kasar tare da rashin gudanar da shugabancin da ya dace da al'ummar da suke mulka.

Yana mai cewa lokaci yayi da zasu yi anfani da abubuwan da suka koya da zummar maida kasar zuwa kan tafiya mai kyau. Ya zargi 'yan siyasa da bata dimokradiya.

A cewar Arziki lokacin zabe ana neman mutanen da zasu yi aiki ne bisa ga gaskiya ba masu kudi ba. Yace zasu sa mutane bisa hanyoyin kyautata rayuwarsu ba sai sun jira wani ya basu abu ba. Yace su ne zasu gaji shugaban kasar na yanzu idan lokacin mulkinsa ya kare.

Sai dai 'yan jam'iyyar PNDS mai mulki irin su Adamu Manzo dan jam'iyyar yace Allah ya kaimu 2021 a ga wanda zai gaji Shugaban kasa Issoufou Mahammadou. Yana mai cewa 'yan kungiyoyin fararen hula ba sa basu tsoro idan sun shiga faggen siyasa.

Adamu Manzo ya musanta zargin cewa 'yan siyasa sun kasa yana cewa kowa ya san aikin da gwamnatin yanzu tayi kuma tana kan yi.

A saurari rahoton Souley Barma don karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kungiyoyin Fararen Hula Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasar Nijar Ta 2021- 3' 20"