A bayan wani jawabin shugaban Koriya ta Arewa, Koriya ta Kudu ta gabatar da tayin tattaunawa da kishiyar tata a kan yiwuwar kyale 'yan wasan Arewa su halarci gasar Olympics na hunturu da za’a yi a Koriya ta Kudu.
Yau Talata ministan yada labarai na kasar, Cho Myoung-gyon, ya ce Koriya ta Kudu tana so ta gana da jakadan Koriya ta Arewa nan da mako daya, a kauyen Panmunjom. Wannan taron zai zama tattaunawar farko a tsakanin kasashen biyu tun watan Disambar shekarar 2015.
Koriya ta Kudu ta bukaci zaman tattaunawar kwana daya a bayan da shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya yi jawabin shigowar sabuwar shekara inda ya sanar da yana tunanin aika tawagar 'yan wasan kasar domin shiga cikin wasannin Olympics na hunturu da za'a yi a kasar Koriya ta Kudun.
Shugaban kasar Koriya ta Kudu Jae-in ya yi maraba da shawarar da Kim ya yi don tattaunawa a ranar Litinin, amma ya ce duk wani ci gaba da ya dace a kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu dole ne ya dace da yin watsi da shirin nukiliyan Koriya ta Arewa.